in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kafa tsarin bunkasa gandun daji nan da shekarar 2050
2018-01-06 12:23:06 cri
Hukumar kula da gandun dajin ta kasar Sin ta shirya wani tsari na bunkasa kamfanonin dake kula da al'amurran gandun dajin kasar da kuma kara albarkatun gandun dajin kasar zuwa wani matsakaicin matsayi a duniya nan da shekarar 2050.

Zhang Jianlong, shugaban hukumar kula da gandun dajin ta kasar Sin shi ne ya tabbatar da hakan, ya ce wannan wani sabon mataki ne da gwamnatin Sin ta dauka na zamanantar da wannan fanni, karkashin jadawalin jam'iyya mai mulkin kasar.

Da ma dai babban taron jam'iyyar kwaminis karo na 19 wanda ya gudana a watan Oktoba, ya yanke shawarar lalibo karin hanyoyin samarwa kasar kyakkyawar makoma, da inganta sha'anin tafiyar da mulki, da bunkasa al'adu, da kuma kawata ci gaban kasar nan da shekarar 2050.

Zhang ya bayyana cewa nan da shekarar 2050, matsayin gandun dajin kasar Sin zai fadada zuwa cubic mita biliyan 26.5, kuma kashi 72 bisa 100 na bunkasuwar harkokin gandun dajin zai samu ne daga bangaren ci gaban fasaha.

Duk da kasancewar kasar Sin ta samu matukar bunkasuwar fannin albarkatun gandun daji mafi sauri a duniya a shekaru 5 da suka gabata, Zhang ya bayyana cewa, fannin gandun dajin yana tafiyar hawainiya ta fuskar ci gaban zamani karkashin shirin zamanantar da bangarorin kasar Sin.

Ya ce karancin albarkatun gandun daji na daga cikin mahimman batutuwan da suka haifar da koma baya ga ci gaban muhallin halittu da kuma karanci albarkatun da ake samu daga bangaren muhallin halittun, in ji Zhang.

Ya ce domin samar da ingantaccen yanayi, hukumar kula da gandun dajin ta kasar Sin ta rarraba shirye shiryen zamanantar da sashen gandun dajin zuwa bangarori daban daban. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China