in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na dauke da hekta miliyan 70 na itacen daji da aka shuka mafi yawa a duniya
2016-08-29 10:41:00 cri

Jami'in ofishin gandun daji na Sin mista Zhang Jianlong ya sanar da cewa, kasar tana dauke da hekta miliyan 69.3 na itatuwa da aka dasa wanda ya fi yawa a duniya, yayin da aka shafe sama da shekaru sittin ana aikin dashen. A wani taron 'yan jarida game da cigaban gandun daji da ya shirya a karshen makon jiya a Hohhot, mista Zhang ya bayyana cewa adadin gandun dajin kasar Sin ya fara bunkasa ne tun a farkon shekara ta 1950, inda ya karu daga hekta biliyan 1.24 zuwa hekta biliyan 3.12, kimanin hekta miliyan 208, wannan karin daji ya lulunbe kashi 26.66 daga cikin 100 na kasar, inda sama da shekaru 60 da suka gabata yana kashi 8.6 cikin 100. Ofishin na kokarin ganin an kara dasa itatuwa a cikin jihohin da shirin Ziri Daya da Hanya Daya ya shafa, su ne jihohin Beijing-Tianjin-Hebei, da kuma zirin tatalin arziki a yankin kogin Yantze. Sin ta taka rawar gani wajen yaki da hamada, yayin da yankin hamada ya ja baya sosai a cikin shekaru goma na baya bayan nan. (Laouali Souleymane)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China