in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zimbabwe ya nada mataimaka biyu
2017-12-28 09:02:00 cri

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya nada tsaffin kwamandojin da suka taka rawa a rundunar tsaro da wanzar da zaman lafiya ta mayakan kasar Constantino Chiwenga, da Kembo Mohadi a matsayin mataimakan sa biyu.

Wata sanarwa da aka fitar ta bayyana cewa, nadin da shugaban ya yi wa jami'an biyu, da rantsuwar kama aiki da za su yi a Alhamis din nan, sun dace da tanajin kundin mulkin kasar.

Hakan dai na zuwa ne bayan da a baya aka nada mutanen biyu a matsayin sakatarori a jam'iyyar Zanu-PF mai mulkin kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China