Kasashen nahiyar Afirka sun yi kiran da a bullo da wata yarjejeniya da za ta dace da muradun kasashe masu tasowa, a matsayin wata kafa ta kawar da shingen cinikayya da kasashen suka shafe kimanin shekaru 15 suna fuskanta
Babban sakatare a ma'aikatar harkokin kasashen waje ta kasar Kenya Karanja Kibicho ne ya bayyana hakan yayin taron ministocin kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO a takaice da ke gudana yanzu a haka a kasar Kenya.
Ministocin kasashen da ke halartar wannan taro da suka hada da na Benin, Burkina Faso, Chadi da Mali, sun amince cewa, muddin ba a cimma yarjejeniyar da za ta kai ga kawar da rangwame kan amfanin gona a taron na birnin Nairobin Kenya ba, hakika za su nemi yin hakan a gaban kotu.
Ministan harkokin tattalin arziki na kasar Chadi Aziz Mahamat Saleh ya ce, idan har aka cimma wannan yarjejeniya ta kawar ta rangwame kan amfani gano, hakan zai taimaka wajen samar da daidaito a nahiyar Afirka, lamarin da zai kara taimakawa kasashen amfana da sassan cinikayya cikin 'yanci.
Mahalarta taron na Kenya sun amince cewa, dandalin na WTO, shi ne dandalin da ya dace ga kasashe na Afirka da ragowar masu ruwa da tsaki, wajen samun dabarun da suka bukata ta yin gogayya a harkokin cinikayya.(Ibrahim)