in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CICC: Sin na shirin zama kasar da ke kan gaba wajen shigo da kayayyaki a duniya
2017-12-05 10:46:11 cri

Wani sabon rahoto da kamfanin kula da harkokin zuba jari na kasa da kasa na kasar Sin (CICC) ya fitar a jiya Litinin na nuna cewa, nan da shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin za ta sha gaban kasar Amurka na zama kasar dake sahun gaba wajen shigo da kayayyaki a duniya.

Rahoton ya ce, a cikin shekaru goman da suka gabata, matsakaicin alkaluman shigo da kayayyaki na kasar Sin ya zarta na Amurka da kaso 6 cikin 100. Don haka, rahoton ya ce, idan har tazarar ta ci gaba da kasancewa a haka a shekara ta 2018 da ke tafe, sannan matsakaicin makin ya kai kaso 0.15 cikin 100 a shekarun dake tafe bisa halin da ake ciki, kasar ta Sin za ta kasance kasar dake kan gaba wajen shigo da kayayyaki a duniya nan da shekaru 2022, za kuma ta ci gaba da rike wannan kambu nan da shekarar 2025.

Har ila rahoton na CICC ya ce, yanzu haka kasar Sin ce ke kan gaba a duniya a fannin fitar da hajoji zuwa ketare a duniya, kana ta biyu a fannin shigo da kayayyaki. Yadda kasar take shigo da kayayyaki ya yi matukar tasiri a duniya, duba da cewa, ita ce take kan gaba wajen fitar da kayayyaki zuwa kasashe da yankuna 41, idan aka kwatanta da Amurka wadda ke fitar da hajojinta zuwa kasashe 36 kawai.

Idan har kasar ta Sin ta ci gaba da fitar da hajojinta zuwa kasashen ketare a 'yan shekaru masu zuwa, babu tantama harkokin cinikayyar kasar zai kara daidaita kamar yadda lamarin yake a shekaru biyun da suka gabata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China