in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kekunan kasar Sin da suka dace da muhalli za su shiga nahiyar Afrika
2017-12-05 09:16:56 cri

Za a kaddamar da amfani da kekunan kasar Sin da suka dace da kare muhalli a Afrika, wadanda za a iya zirga-zirga da su cikin birane yayin da zai rage cunkoso da hayaki mai gurbata muhalli.

Kekunan hayar wanda kamfanin Mobike ya kirkiro, dake amfani da manhajar waya na rage cunkoso tare da inganta rayuwar birni.

Shugaban sashen kulla hadin gwiwa na kamfanin Mobike Florian Bohert, ya ce kamfanin zai kaddamar da kekunan a birnin Nairobin Kenya cikin shekara mai zuwa, sannan daga bisani a kaddamar a sauran kasashen Afrika.

Ya ce, suna da niyyar kaddamar da kekunan a nahiyar, da zarar sun cimma yarjejeniya da hukumomin birnin Nairobi domin warware matsalolin birnin.

Florian Bohert ya ce, kekunan sun dace da kare muhalli da kuma kiwon lafiya saboda suna rage cunkoso da gurbatar muhalli a birane.

Ya kara da cewa, kekunan na rage yawan fili da ake mamayewa domin mota daya na zaman kekuna 10, yana mai cewa, kekunan na da dadin amfani da kuma sauri.

Tuni ake amfani da kekunan a biranen kasar Sin da Amurka da Jamus da Italiya da Singapore da sauransu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China