in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta soke mukamin farin jakada da ta baiwa Mugabe
2017-10-23 10:39:41 cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar da janye sabon mukamin farin jakada da ta baiwa shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, mukamin da ta baiwa Mugabe a matsayin mai kokarin yaki da cutukan da ba'a daukarsu ta hanyar iska wato NCDs a nahiyar Afrika.

A Juma'ar da ta gabata ne WHO ta ayyana ba da lambar yabon na farin jakada ga shugaba Mugabe, bisa la'akari da abin da ta ce yunkurin da gwamnatinsa ke yi wajen yaki da cutukan NCDs.

Darakta janar na hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, ya saurari mabanbantan ra'ayoyin jama'a game da wannan batu, inda wasu da dama suka nuna rashin gamsuwa da bayar da wannan mukami.

To sai dai kuma, bayan da hukumar ta tuntubi gwamnatin Zimbabwe, Tedros ya ce, daga bisani sun yanke shawarar soke mukamin a matsayin abu mafi dacewa.

Bugu da kari, gwamnatin Zimbabwe ta sanar da cewa, tuni shugaba Mugabe ya yi na'am da matakin da hukumar ta WHO ta dauka.

Ministan harkokin wajen kasar Walter Mzembi, ya bayyana cewa, matakin da hukumar ta dauka ba zai haifar da wata illa ga Mugabe ba, kuma zai ci gaba da gudanar da aikinsa na wayar da kai game da cutukan na NCDs.

Ministan ya kara da cewa, matakin zai kasance hasara ce ga hukumar WHO a maimakon kunyatarwa ga Mugabe.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China