Jirgin saman kamfanin sufuri na Hainan dake nan kasar Sin, mai lamba 497, ya yi tafiyar sama da kilomita 11,000, yana amfani da wani nau'in man da ba na dangin albarkatun fetur ba.
Jirgin kirar Boeing 787 Dreamliner, ya tashi daga birnin Beijing na kasar Sin, ya kuma sauka a filin jirgin saman O'Hare dake birnin Chicagon kasar Amurka da misalin karfe 12:05 na ranar Talatar nan bisa agogon Chicago. Ya kuma yi wannan tafiya ne ta hanyar amfani da wani nau'in mai da aka sarrafa daga gurbataccen man girki.
Hakan dai wani mataki ne na bunkasa hadin gwiwar Sin da Amurka, a fannin bincike, domin kaiwa ga amfani da nau'o'in mai da ake tatsa daga tsirrai ko halittu masu rai, maimakon dangogin fetur da aka saba amfani da su.(Saminu)