A cewar wani tsarin aiki da hukumar kula da yawon bude ido ta kasar Sin ta fitar, aikin na tsawon shekaru 3 zai bada damar samar da bandakuna masu kyau da tsafta wadanda za su rika kulawa daidai-wadaida.
Wannan na zuwa ne gab da kammala shirin kula da bandakuna na 'Toilet Revolution' da aka kaddamar a 2015, wanda aka kashe yuan biliyan 20 kwatankwacin dala biliyan 3 wajen samarwa ko gyara bandakuna 68,000 a wuraren yawon bude ido, adadin da ya dara bandakuna 57,000 da aka kayyade.
Shugaban hukumar Li Jinzao, ya ce shirin Toilet Revolution na da muhimmanci gaya, wajen daga darajar yawon bude ido. (Fa'iza Mustapha)