in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe mutane 26 a harin da aka kai wata majami'a a Texas ta Amurka
2017-11-06 09:37:22 cri

Gwamnan jihar Texas ta kasar Amurka Greg Abbott ya ce, kimanin mutane 26 ne suka mutu galibi daga masu shekaru 5 zuwa 72, bayan da wani dan bindiga ya bude wuta kan masu Ibada jiya Lahadi a majami'ar Sutherland Spring dake jihar ta Texas.

Da yake yiwa manema labarai karin haske kan lamarin, babban lauyan jihar Texas Ken Paxton, ya ce dan bindigan ya shiga cikin majami'ar ce da misalin karfe 11 da rabi na safe, agogon jihar ta Texas inda ya bude kan taron jama'a.

A cewar kwamishinan yankin Wilson Larry Wiley, jami'an tsaron sun yi nasarar harbe dan bindigar daga nisan kimanin kilomita 9 daga yankin Guadalupe bayan da aka yi masa kofar rago.

Mai magana da yawun asibitin jami'ar San Antonio Leni Kirkman ta ce , mutane a kalla 8 ne aka yiwa magani. Ko da yake rahotanni daga yankin na Wilson sun ruwaito wani jami'in tsaro mai suna Sheriff Joe Tackitt na cewa, mutane da dama ne suka jikkata sanadiyar harin wanda wani mutum mai suna Devin Kiley mai shekaru 26 da haihuwa ya kaddamar ta hanyar amfani da babbar bindiga, yana kuma sanye da rigar da harsashi bai ratsa ta. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China