in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asibitin tafi da gidan na jirgin ruwan kasar Sin ya kai ziyara a Kongo Burazaville
2017-10-11 11:18:59 cri
Jiya Talata, asibitin tafi da gidan na jirgin ruwan kasar Sin wato Peace Ark, ya isa tashar jiragen ruwa ta Pointe-Noire ta kasar Kongo Brazaville, don fara ziyarar sada zumunci na kwanaki 8 a kasar, tare kuma da ba da taimakon jinya na jin kai a kasar.

Wannan ne karo na farko da jirgin ruwan na sojojin ruwan kasar Sin ya kai ziyara a kasar Kongo Brazaville.

A yayin gagarumin bikin maraba da zuwan sa, ministar kula da harkokin kiwon lafiya da al'ummar kasar Jacqueline Lydia Mikolo ta ce, kasarta tana mayar da hankali sosai kan ziyarar jirgin ruwan Peace Ark, wadda ta nuna dangantakar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu. A yayin ziyarar, jirgin ruwan zai gudanar da aikin jinya ga jama'ar kasar Kongo Brazaville, wannan ya nuna cewa, ba kawai kasashen biyu na da kyakkyawar dangantaka a tsakanin gwamnatocinsu ba ne, hakan yake ne a tsakanin jama'ar kasashen biyu.

A yayin ziyarar, jirgin ruwan Peace Ark zai ba da jinya ga masu bukata, ban da wannan kuma, zai aika wasu kungiyoyi zuwa asibitocin kasar, don samar da hidimar jinya. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China