in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Kenya ya yi kira ga 'yan kasar da su zauna lafiya gabanin zaben shugaban kasar da za a sake
2017-10-23 09:22:40 cri

A jiya Lahadi ne shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya ya yi kira ga daukacin 'yan kasar da su zauna lafiya gabanin zaben shugaban kasar da za a sake maimaitawa ranar 26 ga watan Oktoban wannan shekara.

Shugaba Kenyatta wanda ya yi wannan kiran yayin da yake jagorantar addu'ar neman zaman lafiya, ya kuma bukaci masu kada kuri'u da su fito kwansu da kwarkwartansu domin zabar dan takarar da suke so yayin zaben shugaban kasar, kana da kada su bari 'yan siyasa su yi amfani da su su tayar da fitina.

Kalaman shugaban na zuwa ne, bayan da jagoran 'yan adawar kasar Raila Odinga ya janye daga zaben, inda ya yi kira ga magoyan bayansa da kada su shiga zaben shugaban kasar da ake shirin gudanarwa.

Sai dai shugaba Kenyatta ya ce, babu gudu babu ja da baya, duk da bayanan da shugaban hukumar zaben kasar ta Kenya ya yi a makon da ya gabata cewa, hukumar ba ta da tabbas game da gudanar da zabe mai adalci. A makoni biyun da suka gabata dai, shugaba Kenyatta ya ci gaba da yakin nemansa, inda ya ziyarci yankunan da ya fi karfi, har ma da na abokin hamayyarsa domin ya kara samun magoya baya.

Amma jagoran 'yan adawa Raila Odinga ya hakikance cewa, ba za a gudanar da zaben na ranar 26 ga watan Oktoba ba, har ya bukaci jama'a da su gudanar da zanga-zanga a fadin kasar a wannan rana.

Rarrabuwar kauwannan da ake samu, ya kara haifar da zaman dar-dar a sassan da dama na kasar ta Kenya, inda shugabannin jam'iyyun adawa (NASA) da bangaren jam'iyya mai mulki ke musayar zafafa kalamai a tsakaninsu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
ga wasu
v An tsai da ranar sake zaben Kenya 2017-09-05 08:49:27
v Kenya: An tanaji na'urorin kada kuri'u na zamani 2017-06-13 09:14:08
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China