in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya: An tanaji na'urorin kada kuri'u na zamani
2017-06-13 09:14:08 cri

Hukumar shirya zabuka mai zaman kan ta, da lura da kan iyakokin kasar Kenya, ta ce ta tanaji tarin na'urorin zamani na gudanar da zabe masu amfani da hidimomi daga tauraron dan adam.

Daraktan sashen harkokin fasahar sadarwa a hukumar Christopher Msando, ya ce na'urorin 35,000 da aka sayo sun riga sun isa cikin kasar, yayin da suke dakon karin wasu na'urorin 10,000 nan gaba cikin mako mai zuwa.

Kaza lika an tanaji karin wasu na'urorin na ko ta kwana 4,000, an kuma horas da ma'aikata da dama dabarun amfani da na'urorin, yayin babban zaben kasar dake tafe cikin watan Agusta mai zuwa.

Mr. Msando ya ce, na'urorin da za a yi amfani da su yayin zaben na da kariya ta musamman, duba da cewa suna aiki ne da tauraron dan adam, wanda hakan zai dakile yunkurin masu sace kayan zabe. Ya ce, babban burin da aka sanya gaba dai shi ne gudanar da sahihin zaben cikin kwanciyar hankali da lumana a daukacin fadin kasar ta Kenya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China