in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samu habakar kudaden shiga da na aiwatar da ayyuka
2017-10-17 10:01:11 cri

Ma'aikatar harkokin kudi ta kasar Sin, ta ce bisa karfin tattalin arzikin kasar, kudaden shiga da take samu, da kuma wanda take kashewa na gudanar da ayyukan raya kasa na samun tagomashi yadda ya kamata a cikin rubu'i ukun farko na bana.

Ma'aikatar ta ce, a cikin watanni 9 farko na bana, kudin shigar ya karu daga kaso 9.7 bisa dari na makamancin lokacin a bara, zuwa trilliyan 13.41, kwatankwacin dala trilliyan 2.

An samu wannan kari ne daga kudin haraji da kasar ke samu, wanda ya karu da kaso 12.1 bisa dari zuwa yuan triliyan 11.31.

Har ila yau cikin wadancan watanni, kudaden da ake kashewa na aiwatar da ayyukan raya kasa sun tashi da kaso 11.4 bisa dari zuwa yuan triliyan 15.19, inda gwamnatocin tsakiya da na yankuna ke aiwatar da kunshin kasafin kudin bana cikin sauri fiye da bara.

Yadda tattalin arziki ke samun tagomashi ba tare da tangarda ba ya gina wani tubali na samun kudin shiga tare da ayyukan raya kasa.

Alkaluman tattalin arziki na GDP a kasar Sin ya karu zuwa kaso 6.9 bisa dari cikin rubu'i na 2 na bana, wanda ya dara kan na rubu'in farko da kuma hasashen da gwamnati ta yi na samun kaso 6.5 bisa dari.

A ranar Alhamis mai zuwa ne kasar za ta fitar da alkaluman tattalin arziki na rubu'i na 3. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China