in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fararen hula 163 sun mutu, kana 91 suka bace yayin wasu hare-haren ta'addanci da aka kai arewacin Myanmar
2017-09-27 11:07:15 cri
Wani rahoto da mahukuntan kasar Myanmar suka fitar na nuna cewa, kimanin fararen hula 163 ne suka mutu kana wasu 91 kuma suka bace, sakamakon wasu hare-haren ta'addanci na baya-bayan da aka kaddamar a jihar Rakhine a karshen watan Oktoban shekarar da ta gabata.

Da yake karin haske kan wadannan alkaluma, mataimakin kwamishina a sashen gudanar da harkokin mulki a gundumar Maungtaw U Ye Htut, ya ce daga ranar 9 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata zuwa 24 ga watan Agustan wannan shekara daga cikin wadanda suka mutu, sun hada da kauyawa 79, da ma'aikatan gwamnati da jami'an tsaro, baya ga wasu mutane 37 da har yanzu ba a ji duriyarsu ba.

Haka kuma an kashe mutane 84 wadanda suka hada da 'yan kabilar Hindu, da na Rakhine, Daingnet da kauyawan Mro, da ma'aikatan gwamnati da jami'an tsaro, kana wasu mutane 54 kuma sun bace a lokacin da dakarun kwatar 'yancin Arakan Rohingya (ARSA) suka kaddamar da sabbin hare-hare daga ranar 25 ga watab Agusta zuwa 26 ga watan Satumban wannan shekara.

A makon da ya gabata ne tawagogin dake tattara bayanai suka fara aiki domin sanin yawan mutanen da suka mutu da barnar da hare-haren ta'addancin suka haddasa a jihar dake arewacin kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China