in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Myanmar ta sami gawawwaki 62 na fasinjojin jirgin saman jigilar rundunar soja da ya yi hadari
2017-06-12 14:57:44 cri
A yau Litinin 12 ga wata ne ofishin kwamandan rundunar sojan Myanmar ya ba da sanarwar cewa, an riga an sami gawawwaki 62, na fasinjojin jirgin saman jigilar rundunar soja da ya yi hadari a ranar 7 ga wata.

A ranar 7 ga watan da muke ciki ne dai wani jirgin saman jigila na rundunar soja mai dauke da fasinjoji 122 ya yi hadari, a kan hanyarsa daga birnin Mergui zuwa na Yangon. A kuma ranar 8 ga wata, rundunar sojan Myanmar ta sanar da fara aikin laluben tarkacen jirgin saman, da kuma gawawwakin fasinjojin dake cikinsa. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China