in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barack Obama ya sanar da soke takunkumin da Amurka ta sanya wa kasar Myanmar
2016-10-08 13:22:42 cri

A jiya Jumma'a ne shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ba da umurnin soke dokar ko-ta-kwana da kasar Amurka ta kakabawa kasar Myanmar, lamarin da ya sheda cewa, Amurka ta soke takunkumin da ta sanya wa kasar.

A jiyan ne dai ma'aikatar kudin Amurka ta bayar da sanarwar cewa, bayan dakatar da dokar ko-ta-kwanan, Myanmar za ta kubuta daga takunkumi a fannonin tattalin arziki, da sha'anin kudi, wadanda a baya ma'aikatar ke sanya ido a kai.

Bugu da kari, mukaddashin mataimakin ministan kudin Amurka Adam Szubin, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, soke takunkumi ga kasar Myanmar a fannonin tattalin arziki, da sha'anin kudi, zai taimaka wa kasar wajen raya cinikayya da tattalin arziki.

Kaza lika ma'aikatar kudin Amurka za ta ci gaba da hadin gwiwa tare da Myanmar, wajen daukar tsauraran matakan yaki da halasta kudin haram, domin tabbatar da tsaron hada-hadar kudade a kasar.

Tun a shekarar 1997 ne dai Amurka ta kaddamar da takunkumi kan kasar Myanmar. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China