in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron kara yin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa a kasar Congo Brazaville
2017-09-26 10:27:03 cri

A jiya Litinin ne, kungiyar karfafa hadin gwiwar kasashe masu tasowa ta shirya wani taron kara wa juna sani kan batun zuba jari da cinikayya a birnin Brazaville, hedkwatar jamhuriyar Congo, inda kamfanonin kasashen Sin da Congo Brazaville suka tatattauna kan sana'o'insu. Wannan ne karo na uku da kungiyar karfafa hadin gwiwar kasashe masu tasowa ta shirya irin wannan taro bayan wadanda suka gudana a kasashen Kamaru da Kwadivwa. Mr. Lv Xinhua, shugaban kungiyar ya bayyana cewa, ana fatan a karshen wadannan taruka za a ingiza kamfanonin kasashen Sin da Afirka su kara yin hadin gwiwa a fannonin samar da kayayyaki da makamashi.

A watan Agustan shekarar 2014 ne aka kafa wannan kungiyar karfafa hadin gwiwar kasashe masu tasowa, kungiya ce mai zaman kanta, kuma ba ta samun riba ba. Nauyin da aka dora mata shi ne karfafa dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasar Sin da sauran kasashe masu tasowa, domin karfafawa kamfanonin kasar Sin gwiwar zuba jari a ketare da kuma kara yin hadin gwiwa da takwarorinsu na ketare a fannonin samar da kayayyaki da makamashi. Mambobin kungiyar sun hada da tsoffin jakadu da manyan jami'an difloamsiyya wadanda suka yi ritaya shekeru 3 da suka gabata, kuma suka taba kulawa da harkokin tattalin arziki da cinikayya, tare da kamfanoni kusan 130. Mr. Lv Xinhua yana mai cewa, "Kasashen Afirka dukkansu kasashe ne masu tasowa. Sakamakon haka, kara yin hadin gwiwa tsakaninsu tana da muhimmanci matuka. Yanzu ana yin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa a fannoni iri iri, kamar fannonin siyasa da tattalin arziki da al'adu da kimiyya da fasaha da ilmantarwa da dai makamatansu. Nauyi mafi muhimmanci da aka dora wa kungiyarmu ta karfafa yin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa shi ne taimakawa karin kamfanoninmu wajen neman ci gaba a ketare. Manyan jami'an diflomasiyya da dama da suka ritaya su ne mambobin kungiyarmu, za su taimaka sosai."

Mr. Lv Xinhua ya bayyana cewa, a yayin tarurukan kara wa juna sani a fannonin zuba jari da cinikayya da kungiyar ta shirya a kasashen Kamaru da Kwadivwa da Congo Brazaville, kamfanonin kasar Sin sun nuna sha'awa sosai. Daruruwan kamfanoni sun halarci kowane taron da aka shirya. Mr. Zhou Mingfu, babban direktan kamfanin zuba jari na Atobo na Suzhou, kuma mamban kungiyar karfafa hadin gwiwar kasashe masu tasowa ya fara yin hadin gwiwa da kamfanonin kasashen Afirka tun shekarar ta 2002, yana mai cewa, "Hakika, mun gamsu da zama mamban kungiyar karfafa hadin gwiwar kasashe masu tasowa, alal misali, mu kan samu bayanai game da albarkatun kasa, da yawan mutane da abubuwan da suke bukata da kuma abubuwan da za mu iya fitarwa da dai sauransu. Muna son neman ci gaba a kasashen Afirka yayin da ake shigar da makamashin Afirka a kasar Sin."

Mr. Gidas Douniama, tsohon dalibi a jami'ar koyon harsuna da al'adu ta Beijing, shi ne yake kula da harkokin Sin a kamfanin General Insurance na kasar Congo Brazaville, ya iya Sinanci sosai, yana mai cewa, "Ina kula da harkokin da suka shafi inshora na kamfanonin kasar Sin a kamfaninmu. Sabo da haka, shugabana ya turo ni zuwa wannan taron kara wa juna sani. Na ga kamfanonin kasar Sin da yawa a nan, idan suna bukatar inshora, zan iya taimaka musu."

A jiya Litinin ne, wato 25 ga watan Satumban, tawagar wakilan kungiyar karfafa hadin gwiwar kasashe masu tasowa ta kasar Sin da shugabannin kamfanonin kasar Sin fiye da 20 wadanda suke neman ci gaba a kasar Congo Brazaville suka yi taron tattaunawa, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan yadda kamfanonin kasar Sin za su iya tinkarar mawuyacin hali da kalubalolin da suke fuskanta a yayin da tattalin arzikin kasar Congo Brazaville ke cikin mawuyacin hali sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China