in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya taron gabatar da shirye-shiryen hadin gwiwa tsakanin lardin Hebei na kasar Sin da jihar Kaduna ta Najeriya
2017-05-23 11:16:30 cri


 

A makon da muke ciki yanzu, wata tawagar wakilan tattalin arziki da cinikayya ta jihar Kaduna dake Najeriya wadda ke karkashin jagorantar gwamna Nasir El Rufa'i na jihar Kaduna, tana rangadi a lardin Hebei na kasar Sin bisa goron gayyatar da gwamnatin lardin Hebei ta aike mata, domin kokarin karfafa hadin gwiwar sada zumunta tsakaninsu. A lokacin da tawagar ke rangadi a lardin Hebei, ita da hukumar lardin Hebei sun yi hadin gwiwa sun shirya wani taron gabatar da shirye-shiryen yin hadin gwiwa a fannonin masana'antu da makamashi a tsakaninsu, har ma sun daddale wasu yarjejeniyoyin fahimtar juna.

An bayyana cewa, jakadan kasar Sin Mr. Zhou Pingjian, dake Najeriya ne ya gabatar da shawarar yin hadin gwiwa tsakanin larduna masu sada zumunta da kamfanonin mallakar gwamnatin tsakiyar kasar Sin. Wannan shawara ta samu amincewa daga lardin Hebei da jihar Kaduna da kamfanin CCECC. Bisa kokarin da bangarori masu alaka suke yi, yanzu an kafa wani tsarin tuntubar juna, inda lardin Hebei na kasar Sin da jihar Kaduna suka gabatar da wasu shirye-shiryen yin hadin gwiwa tsakaninsu.

1  2  3  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China