in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin yaye daliban kwalejin raya hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa
2017-07-07 10:56:15 cri

Jiya Alhamis ne, ma'aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin da jami'ar Peking suka shirya bikin yaye daliban da suka kammala karatun digiri na biyu a kwalejin raya hadin gwiwar kasashe masu tasowa karo na farko a nan birnin Beijng. Daliban daga kasashe 16 kamar su Timor-Leste da Kambodia da Habasha da wasu jakadun kasashen dake kasar da wakilan hukumomin gwamnatin kasar Sin da malamai da daliban kwalejen kusan 200 ne suka halarci bikin.  

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da kudurin kafa kwalejin raya hadin gwiwar dake tsakanin kudu da kudu wato kasashe masu tasowa a yayin taron kolin da aka gudanar yayin bikin cika shekaru 70 da kafa majalisar dinkin duniya, daga baya aka kafa kwalejin a hukunce a watan Aflilun shekarar 2016, wanda ya karbi dalibai masu neman digiri na biyu da digiri na uku guda 48 a mataki na farko.

A yayin bikin yaye daliban da aka yi jiya, mataimakin ministan harkokin kasuwancin kasar Sin, kana mataimakin wakilin shawarwarin cinikin kasa da kasa na kasar Yu Jianhua ya gabatar da wani jawabi, inda ya bayyana cewa, nan gaba daliban da suka kammala karatu a kwalejin za su kasance dukiyar kwalejin, saboda za su taka muhimmiyar rawa wajen zurfafa hadin gwiwa dake tsakanin kasashe masu tasowa tare kuma da sa kaimi kan ci gaban tattalin arziki a kasashe masu tasowa, Yu Jianhua shi ma ya nuna fatansa ga daliban, yana mai cewa, "Ina fatan bayan da ku ka koma kasashenku za ku kara mai da hankali ga sha'anin gudanar da hadin gwiwa dake tsakanin kasashe masu tasowa, tare kuma da mai da hankali ga kara gina kwalejin, kana ku yada manufofin kwalejin domin kara jawo hankalin dalibai na gari domin su zo nan yin karatu. Yanzu kasar Sin tana hada kai tare da sauran kasashen duniya domin aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, muna sa ran za ku kara kokari domin ciyar da hadin gwiwa dake tsakanin kasashenku da kasar Sin, musamman ma kan ayyukan da suka shafi shawarar ziri daya da hanya daya, ta haka ne za a cimma burin nasarar dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030."

A cikin shekara daya da ta gabata, daliban dake karatu a kwalejin sun yi nazari sun kuma tattauna kana sun kai ziyara wurare daban daban a fadin kasar Sin, sun kuma kalli ci gaban tattalin arzikin kasar Sin cikin sauri, da kyautatuwar zaman rayuwar al'ummar kasar ta Sin a bayyane, sun gano tare da fahimtar fasahohin bunkasuwar da kasar Sin ta samu sosai.

Dalibi Wu Juncheng 'dan kasar Cambodia ya gaya mana cewa, ya samu babban sakamako a kwalejin, zai kuma yi amfani da su a cikin aikinsa a nan gaba, yana mai cewa, "Babban sakamakon da na samu a nan shi ne na koyi fasahohin ci gaban da kasar Sin ta samu, ina ganin cewa, ci gaban kasar Sin ya ba mu mamaki, gwamnatin kasar Sin tana tsara manufofin da suka dace, na ga yadda al'ummar kasar suke kokarin aiki karkashin jagorancin gwamnatin kasar, kana na ga yadda kasar Sin ta kasance daya daga cikin kasashe mafiya saurin samun ci gaba a fadin duniya a cikin shekaru 30 da suka gabata, ina ganin cewa, sauran kasashe suna iya koyon fasahohin da kasar Sin ta yi amfani da su yayin da suke kokarin neman samun ci gaban kasashensu."

Dalili Awan Riak 'dan kasar Sudan ta Kudu ya bayyana cewa, bayan da ya kammala karatunsa a kasar Sin, ya kara gano cewa, abu mafi muhimmaci ga ko wace kasa wadda ke da nufin samun bunkasuwa shi ne ta samu wata dabarar da ta dace da tsarinta na musamman, yana mai cewa, "Na yi karatu a kwalejin, na samu sakamako a zahiri, misali sakamakon da kasar Sin ta samu wajen raya tattalin arziki da raya biranenta, kana na koyi abubuwa da dama dake shafar al'adun kasar Sin, ko shakka babu zan amfana da wadannan."

Shehun malami a jami'ar Peking dake aiki a kwalejin nazari kan bunkasuwar kasashe Zhang Xiaobo yana koyar da darasi ne game da tattalin arziki a kwalejin raya hadin gwiwar kasashe masu tasowa, ya ce, ko da yake wadannan dalibai sun zo ne daga kasashe daban daban, amma dukkansu suna mayar da hankali matuka kan karatu, saboda suna fatan za su yi amfani da ilimin da suke koyo a kwalejin kan aikin da za su yi domin kyautata halin da kasashensu ke ciki. Yana mai cewa, "Na gamsu da kokarinsu, dalibai sun nuna mayar da hankali sosai a kan karatu, wasu suna fatan za su iya kyautata yanayin da kasashensu ke ciki a halin yanzu."

An kafa kwalejin ne a watan Aflilun shekarar 2016 a cibiyar yin nazari kan ci gaban kasa ta jami'ar Peking, makasudin kafa ta shi ne domin horas da kwararrun kasashe masu tasowa.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China