in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Koriya ta Arewa ya jagoranci gwajin makami mai linzami
2016-08-25 10:54:09 cri

Kamfanin dallancin labaran kasar Koriya ta Arewa KCNA, ya bayyana cewa, shugaban kasar Kim Jong Un, ya jagoranci gwajin makami mai linzami da ake harbawa ta jirgin ruwan yaki.

A cewar KCNA, shugaba Kim ya nuna gamsuwa da nasarar gwajin makamin, ya kuma jinjinawa jami'ai da ma'aikata, tare da masana a fannin kimiyya da fasaha da suka taimaka wajen samun nasarar kerawa, da kuma gwajin nau'in makamin na wannan karo.

Shugaba Kim ya ce, kasar sa ta nunawa duniya irin karfin da take da shi na mallakar kayan yaki na zamani, ciki hadda makaman nukiliya, wadanda ka iya kaiwa har sansanonin Amurka dake yankunan Asiya da Pacific.

Daga nan sai ya yi tir da atisayen soji na hadin gwiwar Amurka da Koriya ta Kudu, yana mai cewa, zai dauki matakan da suka dace kan hakan da zarar dama ta samu.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China