in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zhang Dejiang ya gana da shugabar majalisar dokokin kasar Mozambique
2017-02-15 20:40:42 cri

A yau Laraba ne shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang, ya yi shawarwari da shugabar majalisar dokokin kasar Mozambique madam Veronica Nataniel Macamo.

A yayin shawarwarin, Zhang Dejiang ya yi fatan kasashen 2 za su kara hada shirin "ziri daya da hanya daya" da kuma manufofin raya Mozambique wuri guda, za su kuma yi amfani da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashe masu magana da harshen Portugal, ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, da kuma shiyyar masana'antu, wajen inganta hadin gwiwa, a kokarin kara sada wa jama'ar kasashen 2 da alheri.

A nata bangaren, madam Veronica Nataniel Macamo ta ce, majalisar dokokin kasarta, na fatan kyautata mu'amalar sada zumunta da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da kara azama wajen bunkasa hadin gwiwar moriyar juna a tsakanin kasashen 2. Kana a kara taimakawa juna a wurare daban daban, a kokarin ba da sabuwar gudummawa, ta raya dankon zumuncin da ke tsakanin Mozambique da Sin. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China