in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da sabon filin jirgin sama a arewa maso gabashin Kenya
2017-07-24 11:03:51 cri

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya kaddamar da sabon filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa na Isiolo, wanda ke arewa maso gabashin kasar. An dai kaddamar da wannan filin jiragen sama ne a ranar Lahadi 23 ga watan nan.

Da yake jawabi yayin kaddamar da shi, shugaba Kenyatta ya ce, filin jirgin wani bangare ne na shirin fadada harkokin tattalin arziki da yawon shakatawa, karkashin manufar dinke yankunan Lamu dake daura da tashar ruwa ta kudancin kasar Kenya, da kasar Sudan ta Kudu zuwa Habasha wanda aka yiwa lakabi da LAPSSET.

Ya ce, filin jiragen sama na ba da damar bunkasa hada hadar tattalin arziki, da kara samar da guraben ayyukan yi. Kuma wannan sabon filin jiragen da aka kaddamar shi ne irin sa na 5 a kasar.

Wannan filin jirgin sama dai na da fadin sakwaya mita 4,800, yana kuma iya daukar fasinjoji 125,000 a ko wace shekara. Mahukuntan Kenya na fatan zai taimaka wajen safarar hajoji daban daban, da suka hada da naman shanu da sauran kayan lambu, baya ga fadada harkokin yawon bude ido a sassan gabashin kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China