in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi: Habaka bangaren wasanni ya yi daidai da burin kasar Sin
2017-08-28 10:04:45 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga al'umma su bude wasu sabbin bangarorin wasanni domin ba kasar damar zama mai karfi a bangaren wasanni a duniya.

Xi Jinping ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da daidaikun mutane da kungiyoyin wasanni na kasar Sin da suka kunshi kwararru da kuma masu tasowa, tare da wadanda suka samu lambobin yabo yayin wasannin kasa da aka yi karo na 13.

Ya ce, wasanni na samar da wani dandali na samun kasa mai karfi da ci gaba, yana mai cewa, ya kamata a ba batun ciyar da bangaren wasanni gaba muhimmanci, ta hanyar kara kokari wajen shiryawa da aiwatar da sabbin ayyuka.

Yayin ganawar, Shugaba Xi ya ce, an samu gagarumin ci gaba a bangaren wasanni cikin shekaru 5 da suka gabata, ciki har da habakar shirin 'lafiyar jiki ga kowa' da nasarorin da aka samu a wasannin gasa da aka yi a duniya, da kara zurfafa sauyi a bangaren tare da damar karban wasanni motsa jiki da za a yi a lokacin hunturu a shekarar 2022. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China