in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai martaba sarkin Kano ya kammala ziyarar aiki kasar Sin
2017-08-17 20:07:02 cri

Yau Alhamis, rana ce ta karshe a kwanakin ziyarar da mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya gudanar a nan kasar Sin, inda mai martaba da 'yan tawagarsa suka yi tattaki zuwa asusun raya nahiyar Afirka na kasar Sin wato China-Africa Development Fund, da kuma kungiyar bunkasa kasuwanci tsakanin Sin da Afirka, wato China-Africa Business Council a nan Beijing.

Babban manajan asusun raya nahiyar Afirka na kasar Sin, Mista Chi Jianxin ya zanta da mai martaba sarkin Kano, inda mai martaba ya tallata jihar Kano, da kokarin jawo hankalin wannan kamfani don ya zuba jari a Kano dake arewacin Najeriya. A nasa bangaren kuma, Mista Chi ya ce kara fahimtar halin da ake ciki a jihar Kano da ma arewacin Najeriya, inda ya ce, zai duba yiwuwar zuba jari tare kuma da habaka hadin-gwiwa da jihar Kano.

Sa'an nan a ziyararsu ofishin kungiyar bunkasa kasuwanci tsakanin Sin da Afirka, wato China-Africa Business Council, mai martaba sarkin Kano da 'yan tawagarsa sun gana da wakilai daga wasu kamfanoni kanana da matsakaita, wadanda ke da sha'awa ko niyyar zuba jari a kasashen Afirka, musamman a fannonin ma'adinai, gilashi, karfe da sauransu.

A ziyarar aikin ta tsawon kwanaki takwas, mai martaba sarkin Kano gami da 'yan tawagarsa sun ziyarci biranen Guangzhou, da Shenzhen, da Shanghai tare kuma da Beijing, inda suka gana da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar Sin, shugabannin kamfanonin kasar Sin, jami'an diflomasiyyar Najeriya dake kasar Sin, wasu masana tattalin arzikin kasar Sin da sauransu, inda mai martaba ya ganewa idanunsa bunkasa da ci gaban da biranen kasar Sin ta samu, musamman a fannonin tattalin arziki, cinikayya, ababen more rayuwar jama'a da sauransu.

A yayin ziyarar kuma, mai martaba sarkin Kano ya bayyana fatansa na karfafa hadin-gwiwa da mu'amala da kasar Sin, da kara janyo hankalin kamfanonin kasar Sin su shiga Najeriya, su shiga Kano don zuba jari da kafa masana'antu, musamman ta fuskokin saka tufafi, sarrafa takalma da sauransu, domin kyautata zaman rayuwar al'umma da raya tattalin arzikin kasa na Najeriya. Muna iya cewa, kwalliya ta biya kudin sabulu.

Yanzu mai martaba sarkin Kano gami da 'yan tawagarsa sun riga sun tashi daga nan filin jiragen sama na Beijing zuwa gida Najeriya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China