Daga bisa wakilinmu Murtala Zhang ya zanta da mai martaba sarkin, ga cikakkiyar hirarsu.
170815-sarkin-kano-murtala.m4a
|
Wakilinmu Murtala Zhang ke nan a zantarwarsu da mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi II. A yau Talata da yamma ne kuma, ake saran mai martaba sarkin Kano gami da 'yan tawagarsa za su iso nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, zangonsu na karshe a ziyarar da suke a kasar Sin a wannan karo. Kana gobe Laraba, mai martaba sarkin Kano zai gana da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar Sin, inda wakilinmu Murtala zai ci gaba da aiko mana da rahotanni da hirarraki game da wannan ziyara.