in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD na goyon bayan sake farfado da shawarwari tsakanin bangarorin 6 da batun nukiliyar zirin Koriya ya shafa
2017-08-17 10:49:29 cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres a jiya Laraba ya kalubalanci kasar Koriya ta arewa da ta sauke nauyin dake kanta a duniya a dukkan fannoni, tare kuma da gudanar da tattaunawa mai ma'ana bisa kudurorin da kwamitin sulhu ya tsaida, domin sassauta mummunan yanayin da ake ciki a zirin Koriya. A sa'i guda kuma ya kalubalanci bangarori daban daban da batun ya shafa da su warware rikicin ta hanyar siyasa, kana yana goyon bayan sake farfado da shawarwari tsakanin bangarori shida.

Babban sakataren ya bayyana haka ne a jiya yayin taron manema labaru da aka shirya a hedkwatar MDD dake New York, inda ya ce, kwamitin sulhun MDD ya zartas da kuduri mai lamba 2371 a ranar 5 ga watan Agusta, inda aka ba da tabbaci kan nauyin dake kan kasar ta Koriya ta arewa a fannonin tabbatar da zaman lafiya da tsaro. A cewarsa,

'Bisa kuduri mai lamba 2371, tilas ne kasashen duniya su fito karara su bayyana ra'ayinsu na bai daya ga shugabannin kasar Koriya ta arewa, wato kasar ta dauki nauyin dake wuyanta a duniya, tare kuma da sake gudanar da tattaunawa, don sassauta yanayi mai tsanani da zirin Koriya ke ciki.'

Babban sakataren ya bayyana cewa, yanayin da ake ciki a zirin Koriya yanzu haka ya fi na shekaru fiye da goma da suka gabata muni, ya kara da cewa, kuduri mai lamba 2371 da aka zartas baki daya ya samar da wata dama mai kyau wajen warware rikicin ta hanyar diplomasiyya da sake gudanar da tattaunawa. A cewarsa,

'Matakan da za a iya dauka wajen gudanar da tattaunawar suna da yawa, wadanda suka hada da shawarwari a tsakanin bangarori biyu ko shawarwari a tsakanin bangarori shida da batun ya shafa. Sakamakon karuwar tsanantar yanayin da ake ciki a zirin Koriya, ya yiwu za a kara fuskantar matsaloli ta fannonin rashin fahimtar juna, da yanke shawarar da ba ta yi daidai ba da kuma kara tsanantar yanayi. A cikin wannan lokaci, bai kamata ba bangarori daban daban da batun ya shafa su ci gaba da cacar baki, a maimakon haka, ya kamata su gaggauta warware batun ta hanyar diplomasiyya.'

Baya ga haka, Guterres ya bayyana ceewa, a matsayinsa na babban sakataren MDD, zai yi kokarin ganin an aiwatar da kudurorin da kwamitin sulhu ya zartar game da batun zirin Koriya a dukkan fannoni, musamman ma sabon kudurin da aka zartas. Ya ce,

'Ko da yaushe a shirye nake in shiga tsakani kan batun, na kuma sanar da ra'ayi na ga wakilai na bangarorin shida. Zan yi aiki kafada da kafada tare da bangarorin da batun ya shafa, da nufin ba da tallafi a duk lokacin da ake bukata.'

Bugu da kari babban sakataren ya yi kira ga kasashe mambobin MDD da su sauke nauyin dake kansu, a waje guda ya nuna goyon baya ga kasar Koriya ta kudu kan kiran da ta yi wa Koriya ta arewa game da sake hawa teburin tattaunawa. A cewarsa,

'Ina maraba da kasashe mambobin MDD da su ci gaba da shiga wannan muhimmin yunkuri, ina kuma goyon bayan kasar Koriya ta kudu kan kiran ta ga Koriya ta arewa wajen farfado da tattaunawa mai aminci da ma'ana, ciki har da daukar matakai na karfafa amincewar juna don sassauta yanayin da ake ciki, hakan zai taimaka wajen cimma burin tabbatar da kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya.'

Baya ga haka, babban sakataren ya jaddada cewa, dole ne a yi amfani da mataki na siyasa wajen magance ricikin zirin Koriya, maimakon daukar matakan soja, saboda hakan zai haifar da mumunan sakamako. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China