in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi maraba da tuso keyar wadanda ake zargi da aikata laifi daga Kenya
2016-08-10 19:48:13 cri
Kasar Sin ta yi maraba da matakin da aka dauka na tusa keyar mutanen nan 40 da ake zargi da laifin aikata cuwa-cuwa a sashen sadarwa daga kasar Kenya zuwa nan kasar Sin domin su fuskanci hukunci.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta bayyana cewa,wannan mataki ya nuna irin kudurin da kasashen Sin da Kenya suka cimma na ganin bayan masu aikata munanan alaifuffuka a cikin kasashen biyu.

Wata sanarwa da ta rabawa manema labarai bayan da aka tuso keyar mutanen guda 40 a ranar Litinin, 35 daga cikinsu sun fito ne daga babban yankin kasar Sin, yayin da biyar daga cikinsu kuma suka fito daga yankin Taiwan, inda ake tsare da su a ofishin 'yan sanda.

A watan Afrilu ma an tuso keyar wasu mutane 77 da ake zargi daga kasar ta Kenya wadanda suka fito daga babban yankin kasar Sin da kuma yankin Taiwan zuwa nan kasar Sin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China