Ma'aikatar lafiya ta kasar Kenya ta kaddamar da wasu ka'idoji domin tantance sinadaren da ake amfani da su domin dakile karuwar ta'ammali da haramtattun kwayoyi dake ci gaba da yin kamari a kasar
Daraktan sashen kula da magunguna na kasar Jackson Kioko, ya fada cewa, yawan amfani da haramtattun kwayoyi a kasar yana ci gaba da ta'azzara musamman a tsakanin matasan kasar.
Ya yi gargadin cewar, yawaitar ta'ammali da haramtattun kwayoyin babbar barazana ce da ka iya yin nakasu wajen samun nasarar shirin nan na muradin ci gaban kasar nan da shekara ta 2030 da kuma shirin nan na dawwamamman ci gaba na (SDGs), kasancewar matasa su ne kashi biyu bisa uku na yawan al'ummar kasar.(Ahmad Fagam)