in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana samun nasara a shirin samar da yankin ciniki cikin 'yanci a Afrika
2017-07-18 12:42:19 cri

Nahiyar Afrika tana samun nasara a kokarin da take na kafa yankin cinikin cikin 'yanci a ranar 30 ga watan Oktoba, wanda zai shafi kusan rabin kasashen nahiyar dake cikin shirin.

Daraktan cinikayya na Kasuwar bai daya ta yankin gasbashi da kudancin Afrika wato COMESA, Francis Mangeni ya bayyana cikin jawabinsa da aka wallafa jiya a jaridar The Star ta kasar Kenya cewa, kawo yanzu, kasashe 19 daga cikin kasashe 26 dake cikin shirin ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar.

Yankin cinikin cikin 'yanci zai samar da kayayyaki dari bisa dari ba tare da haraji ba na tsawon shekaru 5-8, sai dai kuma, bayan kula yarjejeniyar za a kara cin gajiyar rangwamen harajin da ya kai kashi 60-85 cikin 100. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China