in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECA ta jadadda kira da a magance gibin dake akwai ta fuskar ababen more rayuwa don bunkasa cinikayya tsakanin kasashen Afrika
2017-07-13 10:03:36 cri
Hukumar bunkasa tattalin arziki a Afrika ta MDD ECA, ta jadadda bukatar da ke akwai na magance karancin hanyoyin sufuri a Afrika domin bunkasa cinikayya tsakanin kasashen nahiyar.

Wata sanarwa da aka fitar a jiya, ta ce hukumar ta yi wannan kira ne yayin bude taro kan bada taimako wajen sake fasalin harkokin cinikayya a duniya na 2017, wanda ya gudana a hedkwatar hukumar kula da harkokin cinikayya ta duniya WTO dake Geneva na kasar Switzerland.

Da yake jawabi yayin taron, Darakta a sashen bunkasa ayyuka na ECA Stephen Karingi, ya jadadda bukatar bunkasa cinikayya a tsakanin kasashen Afrika, wanda a yanzu ya tsaya kan kashi 13 cikin 100 na jimilar harkokin cinikayya a nahiyar.

Stephen Karingi ya ce, abun da ECA ke nufi shi ne, akwai bukatar gwamnatocin Afrika su kara zage damtse wajen inganta cinikayya a tsakaninsu, ya na mai alakanta karancin harkokin kasuwanci tsakanin kasashen da rashin cudanya da juna da na isassun hanyoyin sufuri a fadin nahiyar.

A don haka, ya ce ya kamata a yi tunanin inganta hanyoyi sufuri da sauran ababen more rayuwa inda aka fi samun gagarumin gibi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China