in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci Indiya da ta hanzarta kwashe dakarun ta daga kan iyakar kasar
2017-07-06 11:02:21 cri

Mahukuntan kasar Sin sun bukaci kasar Indiya da ta hanzarta kwashe dakarunta da ta jigbe a kan iyakar kasar ta Sin.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang wanda ya bayyana hakan jiya Laraba yayin taron manema labaran da aka saba gudanarwa, ya ce yanzu haka dakarun kasar ta Indiya na yankin kasar Sin kuma hakan babban kuskure ne. Don haka ya bukaci kasar Indiya da ta daidaita wannan matsala cikin ruwan sanya, kana ta samar da yanayin da ya dace na ci gaba da wanzuwar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Geng ya ce, taron da aka gudanar a shekarar 1890 tsakanin Burtaniya da kasar Sin game da yankunan Sikkim da Tibet shi ne ya shata yankin na Sikkim dake kan iyakar kasashen biyu. Kuma dukkan gwamnatocin Indiya da suka gabata sun aminta da wannan yarjejeniya.

Ya ce, matakin baya-bayan nan da kasar ta Indiya ta dauka ya keta dokoki da kudurorin MDD, har ma dokokin kasa da kasa da muhimman muradun hadin gwiwar kasa da kasa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China