in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yanje wasu takardun kudade a Indiya
2016-11-09 10:32:10 cri

Firaministan kasar Indiya Narendra Modi ya bayar da sanarwar janye takardun kudaden kasar na Rupee 500 da kuma 1,000 daga tsarin harkokin kudaden kasar.

Mr Modi ya ce, janyewar ta fara aiki ne tun daga tsakar daren jiya Talata. Sai dai kuma duk wadanda ke rike da wadannan kudade, suna iya saka su a cikin asusun ajiyarsu na bankuna da ofisoshin aikewa da wasiku daga ranar 10 ga wannan wata zuwa 30 ga watan Disamban wannan shekara.

A wani jawabi na musamman da ya gabatar ta gidajen talabijin, firaminista Modi ya ce, an dauki wannan mataki ne da nufin kawo karshen cin hanci da rashawa da yadda mutane ke ajiye kudade ba bisa ka'ida ba, da kuma taka birki ga masu kin biyan haraji.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China