in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNWTO:Yawon bude ido zai samar da ci gaba a Afrika
2017-07-06 09:35:38 cri

Rahoton hukumar kula da harkokin yawon bude ido ta MDD ya ce, yawon bude ido zai iya zama babban abun da zai taimaka wajen samar da dawwamammen ci gaba a nahiyar Afrika.

Rahoton da hukumar ta wallafa a jiya ya ce, idan ta lalubo damarmaki a bangaren yawon bude ido domin ba da gudunmuwa ga samun ci gaba da samar da sauye-sauye da cimman muradun ci gaba masu dorewa, to ya kamata Afrika ta dauki dabarun da za su karfafa cudanya tsakanin al'ummomi, da habaka harkokin yawon bude ido a duniya da kuma inganta zaman lafiya.

Rahoton ya kara da cewa, tsakanin shekarar 2011 da 2014, yawon bude ido ya ba da gudunmuwar dala biliyan 166 ga alkaluman GDP, wanda ya kai kashi 8.5 na tattalin arzikin nahiyar, yayin da ya samar da guraben aikin yi miliyan 21 wato kashi 7.1 na guraben aikin yi a nahiyar.

Daraktan zartarwa mai kula da ayyyuka na hukumar Marcio Favalla, ya ce masu yawon bude ido daga sauran sassan duniya miliyan 58 ne suka ziyarci nahiyar Afrika a bara, wanda ya dara na shekarar 2015 da miliyan 4. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China