in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci gwamnatocin kasashen Afirka da su saukaka harkokin zirga-zirga don bunkasa tattalin arzikin nahiyar
2017-07-06 09:03:26 cri

Hukumar MDD mai kula da raya tattalin arzikin Afirka, ta bukaci gwamnatocin kasashen nahiyar da su bullo da matakan saukaka harkokin zirga-zirga tsakanin al'ummomin kasashen, a wani mataki na bunkasa tattalin arzikin nahiyar baki daya.

Da yake karin haske game da hakan, babban sakataren taron harkokin cinikayya da raya kasashe na MDD (UNCTAD) Mukhisa Kituyi ya bayyana cewa, idan kasashen Afirka suka yi kyakkyawan amfani da bangaren yawon shakatawa da Allah ya hore musu, babu shakka zai inganta rayuwar al'ummomin nahiyar.

Wani sabon rahoton da hukumar ta fitar game da ci gaban tattalin arzikin Afirka na shekarar 2017, ya mayar da hankali kan yadda nahiyar ta yi amfani da sashen yawon shakatawa wajen farfado da tattalin arzikinta.

Alkaluma na nuna cewa, a shekarar 1998 kudaden shigar da kasashen nahiyar suka samu daga kayayyakin da aka fitar a bangaren yawon shakatawa, ya ninka har sau uku daga dala biliyan 14 zuwa kusan dala biliyan 47. Yanzu haka yawon shakatawa ya samar da gudummawar kimanin kaso 8.5 cikin 100 na alkaluman GDPn nahiyar idan aka kwatanta da kaso 6.8 cikin 100 da sashen ya samar a shekarar 1998.

Alamu na nuna cewa, ya zuwa shekarar 2026 sashen yawon shakatawan zai samarwa GDPn nahiyar gudummawar kudaden da suka tasamma dala biliyan 121.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China