in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aikin ginin cibiyar ba da hidima ta helkwatar AU na daf da kammala
2017-04-26 09:26:49 cri

Jami'an hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afrika ta AU, sun yaba da yadda aikin ginin cibiyar ba da hidima da wani kamfanin kasar Sin yake gudana. A jiya Talata ne dai jami'an AUn suka ziyarci katafarer ginin mai hawa 3, wanda ke harabar helkwarar kungiyar dake birnin Addis Ababan kasar Habasha.

Wannan cibiya dai na kunshe ne da sashen tantance ma'aikata da jami'ai, da wuraren cin abinci, da kuma dakunan ajiyar muhimman bayanai da kayan tarihin helkwatar kungiyar.

Da yake bayyana farin cikin sa game da yadda aikin ke gudana, mataimakin shugaban hukumar zartaswar kungiyar ta AU Kwesi Quartey, ya ce aikin na dada haskaka irin kyakkyawar alaka dake wanzuwa tsakanin kungiyar ta AU da kasar Sin. Ya ce, ba wannan ne karon farko da kasar Sin ke gudanar da ayyukan gine gine a helkwatar AU ba.

Mr. Quartey ya kara da bayyana kyakkyawan fatan cewa, Sin za ta ci gaba da tallafawa kasashen Afirka a sassa daban daban, duba da yadda take gudanar da ayyukan raya kasashe da dama, domin samar da ci gaba a fadin nahiyar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China