in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya mika sakon taya murnar kiran taro na biyu na dandalin tattaunawar CICA
2017-06-28 13:45:18 cri

Yau Laraba ne aka kaddamar da taro na biyu, na dandalin tattaunawa na sassa masu zaman kan su, karkashin taron kara mu'amala da kulla dankon zumunci a tsakanin kasashen Asiya wato CICA a nan birnin Beijing, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sako don taya murnar kiran taron.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, tun bayan da kasar Sin ta fara shugabancin taron CICA daga watan Mayu na shekarar 2014, ta sauke nauyin da ke bisa wuyanta, tare da aiwatar da ra'ayin tsaron Asiya yadda ya kamata. Sa'an nan kasar Sin ta kara azama ga aikin tattaunawa game da yadda za a kafa sabon tsarin tsaro da hadin kansu, da inganta hadin gwiwa a fannoni daban daban don kara amincewa da juna, da kyautata tsarin doka na CICA, da kara mu'amala a tsakaninsu, kana da neman samun shawarwari daga jama'a.

Bugu da kari, Xi ya yi nuni da cewa, kiran taron dandalin tattaunawar wanda ba na gwamnati ba wato CICA, wata shawara ce da ya gabatar a yayin taron koli na Shanghai na CICA da aka kira a shekarar 2014.

A watan Mayu na shekarar 2015, an samu nasarar kiran wannan taro a karon farko, wanda ya bude wani sabon shafi na yada hasashen tsaro na CICA, da ma daidaita harkokin tsaro a shiyya shiyya. Yau kuma an kira wannan taro na karo na biyu, inda mahalartan sa za su tattaunawa sosai a tsakaninsu bisa babban taken sa na "Yin kokari don samun tsaro da ci gaban Asiya, yayin da aka cika shekaru 25 da kafuwar dandalin CICA". Shugaba Xi ya yi imanin cewa, taron zai ba da sabuwar gudummawa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali, da ma samun wadata gaba daya a tsakanin kasashen Asiya. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China