in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana kokarin raya makamashi mai tsabta
2017-06-27 13:36:21 cri

Makamashi tushe ne na bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma. A shekaru 5 da suka gabata, Sin ta yi kokarin raya makamashi mai tsabta, da gaggauta canja tsarin makamashi, ta yadda aka kyautata tsarin bunkasuwar tattalin arziki, kana jama'a sun samu karin moriya daga hakan.

A ko wace safiya, malama Zhang 'yar birnin Beijing ta kan hau keke da ake yin hayar sa daga gidanta zuwa tashar jirgin kasa dake karkashin kasa inda ta tafi aiki. Game da keken, Madam Zhang ta bayyana cewa,

"Da farko yana kawo sauki, ana amfani da wayar salula wajen bude shi, irin wannan keken na da yawa. Na biyu suna da araha, ana amfani da shi ta biyan kudi da bai wuce rabin Yuan 1 ko Yuan 1 ba, a kan yi amfani da shi don tafiya aiki ko motsa jiki, ba damuwa da cunkoson motoci, yana da kyau."

Mutane da dama na amfani da irin wannan keke kamar malama Zhang. Ya zuwa watan Mayu na bana, Sin ta ajiye irin wadannan kekuna fiye da miliyan 10 a birane daban daban, kuma yawan mutanen da suke amfani da su ya zarce miliyan 100. A hakika dai, makamashin da a kan yi amfani da shi a kowane lokaci na taka muhimmiyar rawa ga hanyar sufuri.

Ana ajiye na'urar samar da wutar lantarki ta hasken rana mai watt 5 kan irin wannan keke na wani kamfani, wadda kan samar da wutar lantarki ga makullin keken. Si Haijian, shugaban kamfanin Hanergy da ya samar da irin na'urar da suke amfani da ita, yana mai cewa,

"Ban da keke, irin wannan makamashi da kamfanin Hanergy ke samarwa, ya fadada zuwa kasuwanni da ake amfani da shi, kamar a motoci, da jaka, da tanti, har ma da kananan jiragen sama marasa matuki. Yanzu haka muna kokarin yin hadin gwiwa tare da sana'o'i daban daban."

Ban da birane, makamashi mai tsabta yana canja yanayin kauyukan kasar Sin. Ana kiran garin Yongren dake lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin da sunan gari mai hasken rana, albarkatun hasken rana a birnin ya kai matsayi na biyu a daukacin kasar Sin. Shugaban tashar kula da makamashi na kauyuka, a hukumar kula da aikin daji ta garin Yongren Liao Mingrong, ya bayyanawa 'yan jarida cewa, makamashi mai tsabta kamar hasken rana ya kyautata rayuwar jama'a, da kiyaye muhalli gaba daya. Ya kara da cewa,

"Ana da na'urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana kimanin dubu 10, an canja na'urorin dafa abinci a gidaje fiye da dubu 6. Ta haka, an warware matsalar amfani da makamashi a kauyuka, kana an tabbatar da albarkatun daji."

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan sabon makamashin da aka samar ta hasken rana a kasar Sin ya kai matsayin farko a duniya. Mataimakin shugaban hukumar kula da makamashi ta kasar Sin Li Yangzhe ya yi bayanin cewa, makamashi mai tsabta ciki har da hasken rana, zai zama muhimmin kashi a tsarin sabbin makamashin da za a samar a nan gaba. Ya bayyana cewa,

"Makamashin da za a iya samu, muhimmin kashi ne na makamashi da ba na ma'adinai ba a nan kasar Sin, kana tushe ne na kyautata tsarin makamashi na kasar Sin a nan gaba. An yi hasashen cewa, yawan jarin da za a zuba a fannin makamashin da za a iya sakawa daga shekarar 2016 zuwa ta 2020, zai kai Yuan biliyan 2500. Kana ya zuwa shekarar 2020, yawan makamashin da za a samu daga na'urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana, zai zarce kilo watt miliyan 110." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China