in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An raya sha'anin yawon shakatawa a gidajen manoman kabilar Zang
2017-06-23 15:33:16 cri

A yankin kiyaye muhalli na Zecha dake garin Xicang na gundumar Luqu ta jihar kabilar Zang mai zaman kanta,wadda ke Gannan ta lardin Gansu, akwai wani kyakkyawan kauye mai suna Gongquhu.

A shekarar 2012, dan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Gongbao Zhaxi da dansa suka fara karbar baki a gidansu, inda suka zama iyali na farko da ya raya sha'anin yawon shakatawa a gida.

Tare da ci gaban yunkurin raya sha'anin yawon shakatawa a wurin, kauyen Gongquhu ya fara kyautata yanayin da yake ciki, bisa tsarin kauye na zamani.

Yanzu, bisa jagorancinsa, iyalai 12 a cikin kauyen sun kafa kamfanin bunkasa sha'anin yawon shakatawa a gidajensu, da kiwon dabbobi. Masu yawon shakatawa suna iya zama a can, domin samun fahimtar al'adun kabilar Zang yadda ya kamata.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China