Magani irin na yankin Tibet wani muhimmin bangare ne na ilmin likitanci na gargajiyar kasar Sin, mai tarihin shekaru fiye da dubu biyu. Bayan da aka shafe shekaru ana inganta sha'anin, matakan samar da maganin a Diqing ya bunkasa yadda ya kamata. An yi kokarin inganta matakan harhada magungunan yankin Tibet, a daya hannun kuma an kirkiro sabbin fasahohi kan aikin harhada magungunan. (Zainab)