in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun wanzar da zaman lafiya na Congo sun fice daga CAR bayan rahoton MDD na zargin aikata fyade
2017-06-22 10:01:00 cri

Sakamakon binciken da MDD ta yi game da zargin jami'an wanzar da zaman lafiya na jamhuriyar Congo na aikata fyade a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR, rahoton ya gano cewa, matsalar ta sa tuni jami'an Congo Brazzaville sun fara janyewa daga tawagar aikin wanzar da zaman lafiyar ta MDD dake CAR (MINUSCA).

Cikin wata sanarwa da MINUSCA ta fitar a helkwatar MDDr, ta ce, sakatariyar tana ci gaban da yin aikin hadin gwiwa tare da jamhuriyar Congon da kuma MINUSCA domin daukar matakan gaggauta janye jami'an da ake zargin, domin a samu damar aiwatar muhimman ayyukan shirin cikin hanzari.

Akwai zarge zarge masu yawan gaske game da aikata laifukan cin zarafi ta hanyar fyade, da bautarwa, da tilastawa kananan yara wajen shigar da su cikin yaki a CAR, wanda aka gano hakan tun bayan kaddamar da fara binciken a farkon shekarar da ta gabata. Rahoton yana zargin jami'an soji na tawagar wanzar da zaman laifiyar ne da laifukan yin fyade da kananan yara da nufin ba su tallafi ko kariya.

Binciken da MDDr ta yi ya nuna cewa, sake fasalin tura jami'an sojin marasa kayan sarki daga jamhuriyar Congo ya haddasa karuwar zarge zargen aikata laifukan yin fyade da cin zarafi cikin tawagar wanzar da zaman lafiyar a CAR.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China