A yau Alhamis ne a cibiyar harbar tauraron dan Adam ta kasar Sin dake Jiuquan da karfe 11 na safe, kasar Sin ta yi nasarar harba tauraron dan Adam na hangen nesa samfurin HXMT ta hanyar amfani da roka kirar Changzheng 4B. Wannan ne tauraron dan Adam na farko na binciken sararin samaniya mai amfani da na'urar X ray na kasar Sin. Harba wannan tauraron dan Adam cikin nasarar zai taimaka wajen inganta harkar nazarin sararin samaniya na Sin a duniya. (Zainab)