Jama'ar kabilar Tibet dake yankin Diqing mai cin gashin kansa na kabilar Tibet na lardin Yunnan suna da fasahohin hannu na gargajiya da dama na tsawon shekaru fiye da dubu daya. A kan yi amfani da kayan fadi-ka-mutu mai launin baki na kauyen Tangdui, da akwashi na kauyen Shangqiaotou, da tufaffin gargajiya na kabilar Tibet da sauransu a zaman rayuwa na yau da kullum na jama'ar kabilar Tibet. A kokarin bunkasa sha'anin yawon shakatawa na yankin, an fara fitar wadannan kayayyaki zuwa sauran wurare har ma da kasashen waje, ta yadda za a san irin wadannan kayayyaki a sauran sassa na duniya. (Zainab)