in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kasance ta 2 a fannin nazarin kimiya da fasaha a duniya
2016-02-24 10:50:00 cri
Bisa ma'aunin kimiyya da gine-gine na Amurka da asunsun nazarin kimiyya na Amurka ya fidda a farkon wannan shekara an nuna cewa, sha'anin nazarin kimiyya da fasaha na Sin ya ci gaba da kasancewa a sahun gaba a duniya, inda ta zama ta biyu a wannan fanni a duniya.

Kasar Sin ta kasance ta biyu a duniya a fannin kudaden da aka kebe don nazari, yawan kasidun da ke shafar harkokin kimiyya da fasaha da aka wallafa, da ribar da kasar ta samu a fannin kirkire-kirkiren sabbin fasahohi.

Alkaluman na nuna cewa, yawan kudin da aka kebe game da nazari a duniya ya ci gaba da karuwa, musamman ma a kasashen da ke yankin arewacin Amurka, da Turai, da kasashen da ke gabashin Asiya, da kasashen da ke kudu maso gabashin nahiyar Asiya. Amurka ta ci gaba da zama ta farko a fannin harkokin nazari a duniya, yayin da Sin ke biya mata baya, yawan kudin da kasar ta kebe wajen nazari ya yi daidai da na kasashen kungiyar EU baki daya.

Ban da wannan kuma, alkaluma na nuna cewa, bisa yawan kudaden da masana'antu suka kebe game da nazari a cikin dukkan kudaden da kasar ta kebe a shekarar 2013, masana'antun kasashen Sin, Japan da Koriya ta Kudu sun fi kebe kudade, inda wannan adadi ya kai kashi 75 cikin 100.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China