in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Madagascar ta amshi gudumowar kayan abinci tan 4000 daga Sin
2017-06-20 09:49:27 cri

Sama da kayan abinci tan dubu 4 ne gwamnatin kasar Sin ta baiwa kasar Madagascar inda shugaban kasar Hery Rajaonarimampianina ya amshi kayayyakin a ranar Litinin a tashar ruwa na Tamatave na kasar.

A lokacin bikin karbar kayan tallafin, shugaban kasar ta Madagascar ya zayyana wasu daga cikin irin gudumowar da kasar Sin ke baiwa kasarsa, daga bangaren ababan more rayuwa, da tura tawagar kwararrun likitoci na kasar Sin zuwa kasar Madagascar, kana ya bayyana cewa, kasar Madagascar za ta iya noma abincin da za ta dogara da kanta sakamakon sabbin irin shukawa da kasar ke samu daga kasar Sin.

A lokacin bikin mika tallafin kayan abincin, jakadan kasar Sin a Madagascar Yang Xiaorong ya bayyana cewa, al'ummar kasar Magadascan za su fita daga cikin matsalar kamfar abinci da take fama da shi sakamakon tallafin abincin da kasar Sin ta ba su.

Shugaban kasar Madagascar da jakadan kasar Sin sun tabbatar da cewa, hukumar kididdigar afkuwar annoba ta kasar Madagascar (BNGRC), za ta tabbatar da cewa, an raba kayayyakin abincin ga magidanta wadanda suke cikin halin matukar bukata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China