in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira da a kara azama wajen cin gajiyar irin shuka masu samar da makamashi na zamani a Afirka
2017-06-14 10:34:38 cri

Wata kwararriya a fannin kimiyya, kuma daraktar nahiyar Afirka a cibiyar samar da hidimomi daga fasahar amfani da tsirrai don makamashi Margaret Karembu, ta yi kira da a kara azama, wajen amfana daga wannan fasaha a nahiyar Afirka.

Kwararriyar wadda ta yi wannan kira, yayin taron gabatar da rahoton dake kunshe da dabarun shigar da wannan fanni cikin kasuwannin nahiyar Afirka na shekarar 1996 zuwa 2016, ta ce rashin mai da hankali daga tsagin mahukunta, na kawo tarnaki ga cimma dunbin gajiyar dake tattare da wannan fanni.

Kwararriyar ta kara da cewa, wannan ne kuma kalubale dake dakike hadin gwiwa da ya dace a ce nahiyar Afirka na yi a fannin, tare da sauran kasashen duniya masu ci gaba.

Ta ce, ya zama wajibi nahiyar Afirka ta kara azama wajen gudanar da bincike, domin tabbatar da an kau da yunwa, da karancin abinci, ta hanyar samar da nau'o'in irin shuka masu nagarta.

Kwararriyar ta kara da cewa, kalubalen da ake fuskanta sun hada da na dokokin kasuwanci marasa inganci, wadanda ke da nasaba da rashin fahimtar sashen, da kudaden da ake kashewa, kafin samun damar shigar da sabbin nau'o'in iri cikin kasuwanni, da ma dari-dari da ake nunawa wajen karbar sabbin irin shuka na zamani.

To sai dai kuma kwararriyar ta ce, hadin gwiwar kasashe masu tasowa a fannin musayar kimiyya, zai baiwa Afirka damar matsawa kusa da kasashe irin su Sin, da Brazil, da Philippines, da Canada da Amurka, ta fuskar cin gajiya daga wannan nau'i na fasahar zamani.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China