in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga kasashen Afirka da su kara kwazo a fannin bunkasa ilimin fasaha
2015-04-28 09:49:21 cri

Mataimakin shugaban kasar Tanzaniya Gharib Mohammed Bilal, ya yi kira ga shugabannin kasashen Afirka, da su mai da hankali ga raya fannin ilimin fasaha, domin kaucewa mummunan tasirin da yawan jama'ar nahiyar ka iya haifarwa a nan gaba.

Bilal wanda ya bayyana hakan yayin wani taron masana da kwararru, game da ilimin fasaha da aka bude a birnin Arusha, ya kara da cewa, akwai bukatar samar da karin kudade domin bunkasa fannonin ba da horon koyar da sana'o'i, domin yaki da rashin ayyukan yi a daukacin nahiyar.

Ya ce, a shekarar 2013, alkaluman kididdiga sun nuna cewa, yawan al'ummar kudu da hamadar Saharar Afirka kadai, sun kai mutane miliyan 926, adadin da ake hasashen zai haura mutane biliyan 2, nan da shekarar 2050. Bilal ya ce, karuwar mutane a dukkanin sassan nahiyar na iya zama babban kalubale, idan har ba a dauki matakan amfana daga hakan ba.

A cewarsa, muddin aka inganta harkar ilimin fasaha da ta koyar da sana'o'i, Afirka za ta ci babbar gajiya daga dimbin al'ummarta a dukkanin fannonin habakar tattalin arziki.

Kimanin fitattun masana, da masu nazari a wannan fanni 100 ne suka harlarci taron na wannan karo, daga jami'o'i da cibiyoyin bincike da dama dake Afirka, da ma na sauran sassan duniya daban daban. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China