in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin Sin sun ba da gudunmuwar abinci ga wadanda fari ya shafa a Kenya
2017-03-13 09:52:09 cri

Goman kamfanonin kasar Sin dake aiki a Kenya sun ba da gudunmuwar kayayyakin abinci da man girki da ruwa ga wadanda fari ya shafa a yankin Makueni dake gabashin kasar.

Da yake jawabi yayin ba da gudunmuwar, shugaban cibiyar kasuwanci na kasar Sin a Kenya, Zhuo Wu, ya ce kamfanonin kasar Sin na da muradin taimakawa wajen shawo kan matsalar fari da ta addabi sassan kasar dake gabashin Afrika.

Ya ce, a shirye suke su taimaka wa jama'ar kasar Kenya da fari ya shafa, inda suka ba su gudunmuwar masara da garin alkama da man girki da kuma ruwa, yana mai cewa, wannan wani bangare na nauyin da ya rataya a wuyansu na karfafa dangantaka da kasar.

Zhuo Wu ya ce, kamfanonin na kasar Sin za su fadada taimakon nasu zuwa sauran sassan kasar dake fama da matsanancin fari.

An kiyasta cewa, jama'ar kasar Kenya miliyan 2.7 ne matsalar fari da ta yi kamari a farkon shekarar nan ta shafa.( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China