in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da tawagar wakilan kawancen dimokuradiyya ta Myanmar
2015-06-11 20:27:59 cri

A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da tawagar wakilan kawancen jam'iyyu kasar Myanmar na NLD dake karkashin jagorancin shugabar tawagar Aung San Suu Kyi a nan birnin Beijing.

A yayin ganawar tasu, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin tana goyon bayan kasar Myanmar a kokarin da ta ke na kare 'yanci da yankunanta, tana kuma mutunta hanyar da kasar Myanmar ta zaba da kanta wajen neman ci gaba.

Har ila yau, tana goyon bayan kasar kan yunkurin neman sulhunta kabilun kasar, haka kuma, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen ciyar da dangantakar dadaddiyar abokantaka da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu gaba.

Kaza kila, kasar Sin tana fatan tare da imanin cewa, kasar Myanmar za ta dukufa wajen bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba.

A nata bangare, Madam Aung San Suu Kyi ta ce, ci gaban dangantakar abokantaka dake tsakanin kasar Sin da kasar Myanmar na da muhimmiyar ma'ana ga kasarta, kawancen jam'iyyu kasar Myanmar na mai da hankali sosai kan dangantakar dake tsakanin Sin da Myanmar, haka kuma, kawancen na girmama nasarori da manyan sakamakon da jam'iyyar kwaminis ta Sin ta samu wajen raya kasa, tana kuma fatan zurfafa dangantakar jam'iyyoyin biyu ta ziyarar tawagar ta wannan karo, da kuma ciyar da dangantakar abokantaka dake tsakanin jama'ar kasashen biyu gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China