in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda na neman a maido mata karin mutanen dake hannu a kisan kare dangi
2016-11-14 10:35:00 cri

Kasar Rwanda ta yi kira ga gamayyar kasa da kasa da ta cafke da kuma tusa keya dukkan mutanen dake hannu kan kisan kare dangi dake gudun hijira a kasashe daban daban zuwa Kigali.

Richard Muhumuza, babban alkalin kasar Rwanda ya bayyana a ranar Lahadi cewa, kwamitin dake sanya ido kan masu gudun hijira na kisan kare dangin Rwanda (GFTU) na ci gaba da gabatar da kararraki kan mutane fiye da 500 da ake zargin su da hannu kan kisan kare dangi dake zaman rayuwa a boye a kasashen duniya daban daban.

Muna godiya ga kasashen da suka hada kai tare da Rwanda, da kuma tusa keyar wadannan mutane masu hannu da jini zuwa kasar Rwanda, kuma muna zaman jira sosai na tuso keyar sauran mutanen zuwa Rwanda domin su fuskanci shari'a, in ji mista Muhumuza.

Muna kira ga kasashen duniya da su yi bincike, su kama, sannan kuma su tuso keyar dukkan masu hannu kan kisan kare dangi da suke zaman rayuwa a cikin kasashensu zuwa kasar ta Rwanda.

Kalaman Muhumuza sun biyo bayan tuso keyar mutane biyu da kasar Holand ta yi zuwa Rwanda a ranar Asabar da yamma. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China